1 Peter 5

1Ina yiwa dattawan da ke cikinku gargadi, ni da nike dan’uwanku dattijo, mashaidin shan wuyar Almasihu, ni kuma mai samun rabo ne daga cikin daukakar daza a bayyana. 2Saboda haka na gargade ku dattawa, kuyi kiwon garken Allah dake tare da ku. Ku kula da su, ba a kan dole ba, amma domin kuna son yin haka, bisa ga yin Allah. Ku kula da su, ba don cin ribar banza ba amma sabo da yardar rai. 3Kada ku zama kamar masu iko akan mutanen dake hannunku, amma ku zama abin koyi ga garken. 4Sa’adda za a bayyana Sarkin Makiyaya zaku karbi rawanin da darajarsa bata dushewa.

5Hakannan, ku kuma samari kuyi biyayya ga dattawa. Dukanku kuyi damara da tawali’u, kuna bauta wa juna, domin Allah ya na tsayayya da mai girman kai, amma yana yiwa masu tawali’u alheri. 6Saboda haka ku kaskantar da kanku karkashin hannuwan Allah mai iko duka domin ya daukaka ku a madaidecin lokaci. 7Ku jibga masa duk taraddadin zuciyarku, domin yana kula da ku.

8Ku natsu, ku zauna a fadake. Magabcinku, ibilis, kamar zaki mai ruri yana zazzagawa, yana neman wanda zai cinye. 9Ku yi tsayayyiyar gaba da shi. Ku yi karfi cikin bangaskiyarku. Ku sani fa abokan tarayyarku da suke cikin duniya suna jimrewa da shan wuyan nan irin taku.

10Bayan shan wuyarku na dan lokaci kadan, Allah mai alheri mara iyaka, wanda ya kiraye ku zuwa ga madawwamiyar daukakarsa cikin Almasihu, zai kammalaku, ya kafa ku, ya kuma karfafa ku. 11Mulki ya tabbata a gare shi har abada abadin. Amin.

12Na amince da Sila amintaccen dan’uwa ne, kuma na rubuto maku a takaice ta hannunsa. Ina yi maku gargadi ina kuma shaida maku cewa abin da na rubuto alherin Allah ne na hakika. Ku kafu a cikinsa. 13Ita matar da ta ke a Babila zababbiya tare da ku, ta na gaisheku, da Markus, dana, yana gaisheku. 14Ku gai da juna da sumbar kauna. Salama ta tabbata a gare ku dukanku da ke cikin Almasihu.

Copyright information for HauULB